Credits

Lyrics

Haba
Na ce ba hakilo ba
Ba zan raina kowa ba
Na Dawayya ɗan Baba
Ban hana huce haushi ba
Haba! Sama
Haba! ashe dai na Gwanja na zama hankaka mai da ɗan wani can na ka
Na zama hankaka mai da ɗan wani can
Aje baya (Haka) a zo gaba aje baya
Aje baya (Sama) a zo gaba aje baya
Ya zama hankaka mai da ɗan wani can
A'a ni na na Gwanja
Ya zama hankaka mai da ɗan wani can
Waɗansu masu sauraro, waɗansu masu yin kallo
Waɗansu na ta yin murna tauraruwarmu ta bullo
Burin wasu su zo gun mu ko ko mu je su sha kallo
Waɗansu ko su zage mu domin muna yabon mata sama
Aje baya (Haka) a zo gaba aje baya
Aje baya (Sama) a zo gaba aje baya
Idan dai batu na daidai ne, kafin in zo akwai farko
Kafin mu doka ganagr nan, waɗansu baya sun doko
Icen kwarai ake dauka a sassaka a katako
Idan kaddara ko ta afka a bi ta ta riga fata haba
Aje baya (Haka) a zo gaba aje baya
Aje baya (Sama) a zo gaba aje baya
Da mun wuce su ce daudu ko ko su ce ɗiyan bisi
Sana'a muke simple kamar ta zana ABC
Yau kuma ga ni na kwashe na bar su babu ko asi
Nai rarrafenga na taka na bar wa makiya rata, haba
Aje baya (Haka) a zo gaba aje baya
Aje baya (Sama) a zo gaba aje baya
Ashe dai hakin da wani ya raina ke tsokane abin kallo
Komai na babba ya fi na yaro, Dawayya kai nake kallo
Tun kan na kai matakin war haka ka saba tara 'yan kallo
Kuma tilas na ga ida kai A Zango ka karfafawa guiwata haba
Ina mata, na ce ina mata
Kai iyeh! ina mata tilas in yaba 'yan mata
Iyah! ba mata ba wa za mu je mu kuranta
Aboki idan ka tara koma gida ka bai mata
Nace akwai kallo tauraruwarku ta bullo
Mata idan kun zo mazan garinku sai sun zo
Da kin kai 'ya wallahi rikonki sai gwarzo
Na ce girman saniya malam a ganta tai tozo
In kin cika 'yar gata Gwanja bikinki sai na zo
Salon rawar mata aje gaba gaba a zo baya
Haba, da ya saura dai Allahu ne ya
instagramSharePathic_arrow_out

Loading...