album cover
Dani dake
1,661
R&B/Soul
Dani dake was released on July 21, 2021 by Amjad Records as a part of the album Alkhairi
album cover
Release DateJuly 21, 2021
LabelAmjad Records
LanguageEnglish
Melodicness
Acousticness
Valence
Danceability
Energy
BPM100

Music Video

Music Video

Credits

COMPOSITION & LYRICS
hamisu said yusuf
hamisu said yusuf
Songwriter

Lyrics

[Verse 1]
Okay, Kashifun Kida, Beats Amjad Records
[Verse 2]
Eh! da ni da ke a duniya ta za mu rayu ko da ba makota
Idan na ce ki zama matata kar ki karya ya zama wauta
Kina ado na zamani
Shin me kike so sanar da ni
[Verse 3]
Na tabbata a duniya nake
Sannan idan zan tuna a rayuwa nake
A kodayaushe tambaya nake
Wane ne ni, wane ne ni da ke nake
[Verse 4]
Na zo gabar da a dole yanzu in tsaya
Idan da hali in ta kara tambaya
Don yanayin da a yau ya mini mammaya
Ya sa jiri wani lokacin hajijiya
[Verse 5]
Ki ce da ni amsata kin sani
Domin kamar da ke kadai mu kai gini
Na rayuwa ta kar na shiga razani
In kin guje mini to wa zai kula da ni
[Verse 6]
Ina tafe, sako da lunguna
Wani lokacin in leka koguna
Da ke kadai na sani cikar muradina
Don ba ki hakuri ma sai in tsuguna
[Verse 7]
Ki zo gare ni don na samu lafiya
Sai kin kusanta za ki saita zuciya
Sai kin kusanta da ni ki saita zuciya
In samu dama don na kara bibiya
[Verse 8]
Domin a gu na kin zamo zinariya
Mai haskaka ni ta kara haska duniya
Ga zahiri ke ce farar zuma
Amma rabon da in gan ki kin ga an jima
Ki agaza duba ina tsuma
[Verse 9]
Sai yaushe ne zan fita wagga kidima
Masoyiya komai don ke nake
Ki tausaya ki so ni ji da ke nake
Sassan jiki da jini da zuci naki ne
[Verse 10]
Na ba ki duk tun kan ki zo ki tambaya
Midget Mix
Written by: hamisu said yusuf
instagramSharePathic_arrow_out􀆄 copy􀐅􀋲

Loading...