album cover
Sai dake
19,518
Dance
Sai dake was released on May 2, 2021 by Amjad Records as a part of the album Sai dake - Single
album cover
Release DateMay 2, 2021
LabelAmjad Records
Melodicness
Acousticness
Valence
Danceability
Energy

Music Video

Music Video

Credits

COMPOSITION & LYRICS
hamisu said yusuf
hamisu said yusuf
Songwriter

Lyrics

[Intro]
Okay! Kasheepun (Sai da kai) ʼkida
[Verse 1]
Kar ki bar ni sahibata
Kar ki ƙi ni, ki fahimta
Sai da ke za na huta
[Verse 2]
Zuciyata ga ke ne ta lallaɓo
Ta amince ki mai da ta ʼyar dako
Kin ga so naki yai min riƙon lago
Wani reshe ya kama ya jijjigo
[Verse 3]
Kin ga ni ban iyawa da so haka
Magani za ki ban don na warraka
Kin ga ya mai da ni wani saɗaka
Ya fi ƙarfina sai yai ta haɓɓaka
[Verse 4]
Kin ga na ba ki raina da zuciya
Me kike so na yi miki zan iya
Yau da ke gobe na shaida tun jiya
Kinga na zam kamar mara lafiya
[Verse 5]
Zuciyata ta nai min bugun tara
Ga shi ni kuma naki na haƙƙura
Duk da na sha wuya ba ni daddara
Kai bala'i na so na da takura
[Verse 6]
Wai ina kika je ne masoyiya?
Na yi nemanki na ƙara tambaya
Har wa ʼyansu su nai mini dariya
Ni ba zan daina sonki ba kin jiya
Duk da ya sani maye ya ɗan giya
[Verse 7]
Tallafa don ki sam minni lafiya
Sai da ke
Sai da ke ne
Sai da ke
Sai da ke ne
Sai da ke
Sai da ke ne
Sai da ke nima zan samu lafiya
Sai da ke
Sai da ke ne
Sai da ke
Sai da ke ne
Sai da ke
Sai da ke
[Verse 8]
Idan kika amsa min so nikuma zan gode miki
Idan kika yarda da ni na san ba ni ba farmaki
Aminta ki bani kula kema kya janye shamaki
Faɗa mini kalmar so ni ita za na biya miki
[Verse 9]
To sai da ke budurwata, sai da ke masoyiya
Sai da ke budurwata, sai da ke masoyiya
Sai da ke, sai da ke, sai da ke ne
Sai da ke, sai da ke, sai da ke ne
Sai da ke, sai da ke
(Midget Mix) Sai da ke, sai da ke, sai da ke ne
Sai da ke, sai da ke
Written by: hamisu said yusuf
instagramSharePathic_arrow_out􀆄 copy􀐅􀋲

Loading...