Credits
PERFORMING ARTISTS
Ali Jita
Performer
COMPOSITION & LYRICS
Ali Jita
Songwriter
PRODUCTION & ENGINEERING
Ali Jita
Producer
Lyrics
[Verse 1]
Sannu sarauniya Rukayya, wanka gun ki za su koya
Gimbiya 'yar dagwas Rukayya, don Allah gabansu juya
Kin zama garkuwa Rukayya, ki yi magana ki tara gayya
Mai halin kwarai Rukayya, ke ce mai dubun masoya
[Verse 2]
Tauraronki na dagawa, mai haske kamar Surayya
Mene ne gimbiya Rukayya, wa ke damun Rukayya
Mai hakuri ina Rukayya, 'yar asali ina Rukayya
Kyakkyawa gambiya Rukayya, wanka sai wajen Rukayya
Akwai tsafta wajen Rukayya
[Verse 3]
Ina buga tambura Rukayya, mata na ta tambaya
Giwa za a bata gulma, lallai babu magiya
Ai in ka ji wance wance ce, domin tai gwagwarmaya
A duba Rukayya gambiya, tun yarinta da tarbiyya
[Verse 4]
'Yar manya 'yar sarakuna, kune ke haska duniya
Dubu ta sha gaban dari, da gani ai babu tambaya
Kura kuma ba ta cin kashin guiwa sai dai ta gwagwaya
Ga dan kolo da malami, sai an raya tsangaya
Yara kun ga Rukayya jaruma, ni dai na ba da inkiya
[Verse 5]
Sannu Rukayya sannu sannu, kowa ke ya wa maraba
Sai nasara da dadawa, sam ba ki san bakin ciki ba
Allah ne yake tsare ki, ba boka da dan Adam ba
Yanzu yabo muke a gun ki, ba kago abin muke ba
Mu yi jita mu sa sarewa, ba zai canzan salon kidan ba
[Verse 6]
'Yan yara na ta harrakawa, manya ma ba a hada ba
Mun tuna tushiya ta dauri, ba zan ce kara ba ce ba
Linzami ya girmi kaza, ko akuya ba ta nada ba
Sama dai ta darar ma yara, sai hange ba sa taba ba
Yanzu Rukayya ce a fili, tauraronta bai dishe ba
[Verse 7]
Ga kainuwa dashen Allah, yanzu Rukayya tafi karfinsu
Mai gado na zinare, ke ce za ki gaji Bilkisu
Ki yi ado na alkyabba mata na kiranki dawisu
Wacce duk ta zage ki lallai zata dinga ni 'ya su
Rukayya ai sarauta ce mata sun fada da bakinsu
[Verse 8]
Masu so su je bude ido nan za su kare kallonsu
Masu so a ba su a basu nan za su mika hannunsu
Sannu dai Rukayya, Rukayyatu gimbiya ta mata
Sannu dai Rukayya, Rukayya jaruma ta matan duniya
Written by: Ali Isah Jita