Music Video
Music Video
Credits
PERFORMING ARTISTS
Ali Jita
Performer
COMPOSITION & LYRICS
Ali Isah Jita
Songwriter
Lyrics
[Verse 1]
Sallama nake Maryam don Allah ki lura
Maryam sarauta ai kin darar wa yara
Maryam mukamanki ba a baiwa yara
A gai da Maryam ga mai sani da lura
Kin dare ma sa a ai kin darar wa yara
Dariya take maryam murmushin hakora
Kin yi kyau zaman falo ki yi zaman kujera
[Verse 2]
Makiyanki Maryam ba tadda ke suke ba
Kin gama da su Maryam ba ta su kike ba
Kainuwa dashen Allah ba ta dan adam ba
Maryam sarauta kun ga ba fushi take ba
Martabobinki ba kadan bane ba
To arzikinki ya bi mki ba da yaudara ba
[Verse 3]
Maryama da ke za ayi ba da su ake ba
Maryama farar rana ba zuwan duhu ba
Maryama akwai ilimi ko ba ku sani ba
Maryama akwai kunya ba kadan ba ce ba
Maryama akwai nazari ba shiru take ba
[Verse 4]
Gimbiya ki sha kurumi duniyarki more
Maryam masoyanki ga su nan a tare
Maryam makiyanki ga su can a ware
Sannu kungiyar giwa kun wuce a kore
[Verse 5]
Maryama sarautar mata akwai kawaye
Maryama rufe kofa babu masu ture
Gaskiya amanar Allah da ba a ture
Maryama sarautar mata nake yabawa
Maryam a gaishe ki kin more iyaye
[Verse 6]
Maryam ku gan ta ita ke share hawaye
Allah ja da ran Maryam ga ta nan a raye
Ci gaba kina sa mu ba ki yi a boye
Za ki sha zuma madara har a ba ki soye
Za ki sanya zinare kin wuce kawaye
[Verse 7]
Maryama sarautar mata nake yaba wa
Maryama sarauta ke kin ka haskakawa
Kin faranta ran bayi ba ki munanawa
'Yar dagwas-dagwas Maryam ta shi ki yi tsayawa
[Verse 8]
Kin wuce a ture ki don yawan tsayawa
To la haula ki sha sosai kin fi mai labewa
Ki yi shiga ta alfarma babu mai hanawa
Ki yi ta mika alkhairi babu ran tsayawa
Wanda duk ya san Maryam za ya tabbatarwa
[Verse 9]
'Ya ta sarauta ce kuma 'yar mulki ce
'Ya ta mutunci ce kuma 'yar dangi ce
Dukkanin yawan taro ke ake ta hange
Ke kina ta yin murna su yi ta zage-zage
Larabawa har Turai duka za ki burge
[Verse 10]
Tafiyarki mike take wance ko a jirge
Sannu ga katangar karfe da ba ta rushe
Duniyar masoya Maryama ta manya
Tarbiya ta koya, hakuri ta koya
Fara'a ta koya dariya ta koya
Ilimi ta koya, taimako ta koya
[Verse 11]
Kare martabarki
Babu mai taba ki
An buga ki an bar ki
Ba a tsokanar ki
Kin gama da boka
[Verse 12]
Ba ta shi kike ba
Kin tsaya ga Rabba
Ba ta wani kike ba
Ke kina da uba
[Verse 13]
Ba ta su kike ba
Maryama babba
Ba ta yara ce ba
Ku taho ku duba
Ba hani ake ba
[Verse 14]
Kyakkyawa Maryam
Ba mummuna ce ba
Na duba Maryam
Ita ba fada take ba
Maryam mai lafiya
[Verse 15]
Ba munafurci ba
'Yar gidan sarauta ba bakuwa bace ba
Sannu 'yar gidan girma Maryam 'yar girma
Sannu 'yar gidan girma Maryam mai girma
[Verse 16]
Zamani yana tashe babu mai hana shi
Ga turare na kamshi babu mai dishe shi
Ga farin wata haske babu mai dishe shi
[Verse 17]
Maryam kenan
Na ce Maryam kenan
Maryam sarauta gaisuwar Ali Jita
Written by: Ali Isah Jita


