album cover
Teacher
1,905
Folk
Teacher was released on December 15, 2021 by 3333646 Records DK as a part of the album Dr. Adamu Dan Maraya Jos Collections
album cover
Release DateDecember 15, 2021
Label3333646 Records DK
LanguageEnglish
Melodicness
Acousticness
Valence
Danceability
Energy
BPM134

Credits

COMPOSITION & LYRICS
Adamu Dan Maraya Jos
Adamu Dan Maraya Jos
Songwriter

Lyrics

Allah karimu mai yi
Sarkin da ba iri nai
Mai gumi da tsari
Allah ka bamu sa'a
Albarkacin ma'aiki
Wanan kidin teacher ne
Wanan batun teacher ne
Teacher uban karatu
Idan ka haifi 'dan ka
Ka kai shi gun karatu
Teacher issa iyanke farce
Sanan ya wanke riga
Ije aji ka gane
Yaro izam karatu
Idan ko 'dan ka
Ya kwana daya
Ya kwana biyu
Bai zo cikin aji ba
Teacher ka gane
Zai bishi har gidan su
Dan iduba lafiya tai
Idan ka haifi 'dan ka
Yayai firamare ai
Yayai sakandare ai
Yaje polytechnic
Yaje University
Yaje Yemen da Russia
Ya gangara America
Sanan ya sauka le
Sanan ya sauka London
Ya gangaro ta Paris
Ya gangaro ta German
Yazo gida kagane
Sanan ya samu aiki
Har yayai gida da moto
Wani teacher ko baida keke
Toh me yasa hakan nan?
Injiniyan gidaje
Masu kera hanya
Masu zane-zane Allah ibasu wanan
Badan akwai teacher ba
Suma basa iyawa ba
Aiki na duniya nan
Daraja ta duniya nan
Mulki na duniya nan
Badan akwai teacher ba
Kowa bazai iya ba
Written by: Adamu Dan Maraya Jos
instagramSharePathic_arrow_out􀆄 copy􀐅􀋲

Loading...