Lyrics

Duniya makaranta Wanda bai sanki ba bai ci gari ba Ka taimakawa mutun in baida shi da dukiyarka kudi ko sutura Kai haka dan Allah ba a hili ba Eh in sanya kaya ko motar hawa Zan hakane in na kai nayi hakan Ban dan kawai in birge wasu ba Ace dani takaran banda shi Bazani takura kaina dan wani ba Zan rayu ba dan in birge wasu ba Ka zama simple shi ne rayuwa Duk wanda ya ce ma baka isa ba Fadarsa banji zata rage ka ba Eh kadauki kanka kamar kowa ka zama mai hakuri Ka zama mai ilimin gane bakin wuri da fari Akokarin ka wuce wane kake sakin asalin hanya Ka saina takura kai wai dan kawai ka birge wani Duk yanda kake akwai mai son yakaika gani Toh idan ka saukaka al'amurranka Rabbi shi zai ma hanya Kudi tufa da abincin ci an kayyade maka shi A zaune ko a tsaye zai zi gareka daina fushi Idan kace zakayi sirrinka kaga toh kabar hanya Ka fara gyara halinka kafin ka gyara wani Rike abinka ka alikimta ka daina duba wani Idan kasa Alkhairi ranka ka riga ka hau hanya Idan ka hadu da mai kinka kai murmushi ya gani Farinciki da nidhadinka haushi yake ya gani Toh kaga in ka rike sirrinka babu mai ja ma jinya Ka gane wan da yake sonka kasan hakan da wuri Ka gane wanda yake kinka kasan hakan da wuri Ka koyi yadda ake hudda da dan Adam in kayi niyya Abinda Rabbi yaban shine abinda zaku gani Abinda bani da shi karya bazan ba dan agani Duk wanda yace zai hakan karshen yana jin kunya Komai nake Allah ne yasa nake natsuwa Wannan yasa komai an kai gareni ban kaduwa Ubangiji in ya zami gatanka babu mai bi ma hanya Duniya makaranta Wanda bai sanki ba bai ci gari ba
Writer(s): Tasiu Abdullahi Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out