album cover
Bayan Mutuwa
7,462
R&B/Soul
Bayan Mutuwa was released on January 1, 2017 by Shareef Studios Invest Nig Ltd as a part of the album Masoya
album cover
AlbumMasoya
Release DateJanuary 1, 2017
LabelShareef Studios Invest Nig Ltd
Melodicness
Acousticness
Valence
Danceability
Energy
BPM184

Credits

Lyrics

Bayan mutuwa ba komai
Daga kai sai halayyar ka
Bayan mutuwa ba komai
Daga kai sai halayyar ka
Da sunan Allah na daya
Sarki mahaliccin duniya
Kaine mai mulkin gaskiya
Wanda sam baka yin murdiya
Kai ka tsara mana duk rayuwa
Muyo kuka ko muyi dariya
Rokon da nake sarki daya
Daura ni a hanyar gaskiya
In bar aikata sabo, yazam bana yin zunubo ko daya
Komai in ka so ni zan zamo
Sam ba wani mai yin kariya
Bukatu na duka na tattaro
Nasan kaine za kayi biya
Nazo neman tuba
Laifukan sabo wanda nayo jiya
Wanda nayo jiya
Laifukan sabo da nayo jiya
Ni abinda ya sani a damuwa
Idan na tuna ranar mutuwa
Ranar da bawa zaya zam mai kishi, yana neman ruwa
Iyaye, ya'ya, ko yan'uwa
Ba wani mai yi maka garkuwa
Dukiya ko mulki ka rike
Suna kallon mai ke faruwa
Yan sanda ko sojoji
Sun zama hoto sannan kuwa
Yanda Allahu yaso zayayi a wannan ranar da rayuwa
In ka mutu ayi maka kuka
Idanu suyi ta zuban ruwa
Idanu suyi ta zuban ruwa
Suyi ta zuban ruwa
Duk soyayyar ka da dangi
Ranar ta kare a gare ka
Bayan anyi maka waka
Zaka ga ana ta saurin kai ka
Yan'uwa abokan arziki
Za su kai ka cikin kabarin ka
A sanya ice a saman ka
Sannan kasa ta biyo bayan ka
Waɗan da suke kaunar ka su za suyo addu'a a gare ka
Su juya suyi tafiyar su, a cikin kabarin ka su barka
Daga nan sai halayyar ka
In kayi mai kyau jindadin ka
In kayi mara kyau halin ka
Rannan ba mai ceton ka
Ba mai ceton ka
Rannan ba mai ceton ka
Kabari ranar farkon gani na dashi na kasa barci
Gaba na sai faduwa yake, na kasa cin abinci
Ba zama ciki ba a juyi, kwanciyar ciki irin na barci
Tsawo, fadi daidai da kai, babu kari domin karamci
Sannan ba hanyar iska da zata zo maka kamar mafici
A cikin kabari da bayani, ba an kai ka bane kayi barci
Mala'iku zasu zo da su'ali, tambayoyi babu ragwanci
Ba sani kuma ba sabo, in kayi daidai ka samu karamci
In ka saba Allah a duniya, daga nan ka fada kunci
Ka fada kunci
Daga nan ka fada kunci
Yan'uwan ka sun manta ka, basa tuna ka a rayuwa
Ayyukan da kai yo masu kyau, su zasu zame maka garkuwa
Dasu za'a dinga tuna ka, jindadi ne gun yan'uwa
Har a dinga yi maka addu'a, sunan ka ba za'ayi mantuwa
Wanda yayi aiki mara kyau, mutuwar sa ba mai damuwa
Kaji wadansu nata fadi "An rage mugun iri a rayuwa"
Ina amfani mummunar shaida? Duba mini yan'uwa
Allah taimaka mani lahira kar in shiga damuwa
Kar in shiga damuwa
Lahira kar in shiga damuwa
Idanu na ta hawaye na tuna ran tsayuwa a gaban gwani
Ranar tonon silili, komai ka aikata sai ka gani
Sharri ko alkhairi ranar mutane duk sai sun gani
Sirrin da kayi shi cikin duhu (Ranar jama'a sai sun gani)
Malaman da suke rufe gaskiya (Ranar jama'a sai sun gani)
Da watan azumi ka sha ruwa (Ranar jama'a sai sun gani)
Kai asiri ka kashe dan uwa (Ranar jama'a sai sun gani)
Ka cinye hakkin marayu (Ranar jama'a sai sun gani)
Mai tauye mudu gun awo (Ranar jama'a sai sun gani)
Ga zina anyi ta a boye (Ranar jama'a sai sun gani)
In fashi da makami shi kayi (Ranar jama'a sai sun gani)
Idan fashi da makami shi kayi (Ranar jama'a sai sun gani)
Maza da suke neman maza (Ranar jama'a sai sun gani)
Mata da suke neman mata (Ranar jama'a sai sun gani)
Ka kashe rai kuma ka sha jini (Ranar jama'a sai sun gani)
Anyo zabe kayi murdiya (Ranar jama'a sai sun gani)
Mai shirka baka da gaskiya (Ranar jama'a sai sun gani)
Shirka babban sabo ne dubiya (Ranar jama'a sai sun gani)
Mace mai ɗaga sauti kan miji (Ranar jama'a sai sun gani)
Wata ta fita babu sani kan miji (Ranar jama'a sai sun gani)
Kuɗin cefane wata ta rage (Ranar jama'a sai sun gani)
Mace mai cutar da kishiya (Ranar jama'a sai sun gani)
Ta bada kan ta ga boka (Ranar jama'a sai sun gani)
Ta sa magani a abinci (Ranar jama'a sai sun gani)
Umm, wayyo Allah (Ranar jama'a sai sun gani)
Wayyo Allah yau tuba nake (Ranar jama'a sai sun gani)
Ni Umar tuba bake Allah
Written by: Umar M Shareef
instagramSharePathic_arrow_out􀆄 copy􀐅􀋲

Loading...