Lyrics
[Intro]
Ayya malam
Auta Waziri kuke ji malam
(Prince production)
[Verse 1]
Kula kin ka bani
Shi ne ya jani
Idan kin ka bar ni
Wa ce za ta so ni
Abun zai yi muni
Idan kin ka gan ni
Dake ni na saba, jini na jikina ʼyar uwa
[Verse 2]
In kina sani shauƙi
Idan za na gan ki
A so ke na ɗauka, ba ta biyunki
Mene kin ka buri, ni za na ba ki
Mu je gun mamana, za na nuna ki ga ʼyan uwa
[Verse 3]
An ce muna kama da ni da ke mun wuce misali
Na san da ba komai ne ba, so ne dalili
Daza mu kauce ʼyan zamba ko masu ƙulli
Mu zamto kamar hanta da jini, soyayyar mu ta zama kainuwa
Eh Allah, ta zama kainuwa
[Verse 4]
Daɗi nake ji idan ki ka ce in zo da ke za mu zauna
Ki na nuna soyayya, tabbas kwai amana
Ba zan saki kuka ba, dukan batu zana tauna
Kamar sai da tana, a bai wa kifi mai mallakin ruwa
[Verse 5]
In ka aje wannan, wa za ya hana ka kai ɗauka
Sirri na so ƙauna, wannan a cikinsa kwai doka
Shi bai wa so yarda shi ne ke sa a gane ka
Sam kar ka lalata, don so ne kaɗai ke sa kai ɗimuwa
[Bridge]
Ayya malam
Kai ɗimuwa
[Verse 6]
In za ki ce ba ki sona
Sai dai idan babu raina
Rana da iska muna nan
Ke ke shiga lammurana
Kin san idan yanzu babu ke, ba ʼyar da zan bai wa ƙauna
Sai in zamto kamar kurma da ban kula kowa
[Verse 7]
Kai idan babu ke, kin san kamar babu ni ne
Daɗin rayuwata, kamar sai da ke ne
Na sanya a rai, ke ɗin garan mallaki ne
I na so mu zauna tare cikin gidana a gobe ki zama uwa
[Outro]
Allah, gobe ki zama uwa
Is prince on the mix
Written by: Auta Waziri


