album cover
Makamashi
589
Afro-Pop
Makamashi was released on July 27, 2023 by Namenj as a part of the album Tuna Baya
album cover
Release DateJuly 27, 2023
LabelNamenj
Melodicness
Acousticness
Valence
Danceability
Energy
BPM169

Credits

PERFORMING ARTISTS
Namenj
Namenj
Performer
COMPOSITION & LYRICS
Namenj
Namenj
Songwriter

Lyrics

[Intro]
Namenj
[Verse 1]
Dashe na tokar shashina
Ga furensa ya yi luf-luf bisa kaina
Da shi na je na yi bankwana
Babu shi cikin rai har ƙalbina
Dashe na so ya yi yabanya
Inuwa ta ganyen dole ta sanya
Ta sa sukuni ga masoya
Inuwa ta ganyen in sun zauna
[PreChorus]
Masoyiya lale-lale
Mu je gida gai da iyaye
Masoyina duba-duba
Ƙaunarka ta sa ni tsumayi
Idan ki na wannan zancen
Kamar na zubda da hawaye
Hawaye
Hawaye
[Chorus]
Makamashin rurin ƙauna
Ya yi garwashi zai ƙone raina
Ka taimaka linzamina
Zo ka agaza ya mai bege na
[Verse 2]
Ka ba ni zobenka masoyi
In saka a hannuna zan juyi
A kanka ni ba na shayi
Alƙawar na ɗauka ni zan nuna
Cininniki ke sa shayi
Shimfiɗa ta ƙauna kar ki yi sauyi
Gwalan-gwatso ni ba na yi
Manufar da ke raina zan nuna
[PreChorus]
Masoyiya lale, lale
Mu je gida gaida iyaye
Masoyina duba-duba
Ƙaunarka ta sa ni tsumayi
Idan ki na wannan zancen
Kamar na ni zubda hawaye
Hawaye
Hawaye
[Chorus]
Makamashin rurin ƙauna
Ya yi garwashi zai ƙone raina
Ki taimaka ya mai so na
Zo ki agaza ya mai bege na
[Outro]
Bege na
Bege na
I say bege na
Bege na
Written by: Namenj
instagramSharePathic_arrow_out􀆄 copy􀐅􀋲

Loading...