Credits

PERFORMING ARTISTS
Ali Jita
Ali Jita
Performer
COMPOSITION & LYRICS
Ali Jita
Ali Jita
Songwriter

Lyrics

Habiba autar mata
Nazo nakewa kidi
Mace mai saukin kai kina da dadin fadi
Zumuwa dole a yarda kinfi karfin madi
Habiba ce bara da yanzu zata kai har badi
Habiba ke kika cinye wadansu sai dai sidi
Duk gida in da Habiba anyi babban hadi
Habiba baiwar Allah nake wa wake
Ku magautanta ku daina sake sake
Ta biyo hanya ku kuna ta yanke
Habiba jita ta nata chanzukan lauka
Habiba in kin zo al'umma sun waraka
Habiba baiwar Allahu shi yake daukaka
Habiba mai haska gida ta haskake har daka
Habiba ce fitila, keka haskakawa
Habiba suna kullum yana dagawa
Ki tajin dadi babu mai hanawa
An jiyo a gabas yamma har arewa
Zamani daidai rigunan sakawa
Habiba giwa kike babu mai musawa
Jinjina miki hannu muke kina rausaya
Jarumar mata kin ci moriyar duniya
Maganar wanka to Habiba dai ta iya
Ina kike Habiba?
Fito kizo Habiba
Adon gari Habiba
Aci ai kiba Habiba
Mai martaba Habiba
Ga haba, haba Habiba
Nasara dubu Habiba
Sitira dubu Habiba
Kwalliya dubu Habiba
Jamma'a dubu Habiba
Yan dubu-dubu Habiba
Da dala dubu Habiba
Maganarki ce Habiba
Wakarki ce Habiba
Ba cekuce Habiba
Ku fada kuce "Habiba"
Nima nace "Habiba"
Kema kice "Habiba"
Suma suce "Habiba"
Allah tsare Habiba
Mai taimako Habiba
Mai dariya Habiba
Mai arziki Habiba
Mai hankali Habiba
Kyauta agun Habiba
Makiyanki zasu bar ki
Dan rabbi ne yabaki
Sanan da kwar jinin ki
Allah kara arzikin ki
A binciken mu sam babu kamar ya ke
Ko wace kawa bukatar ta zama dake
Gadon gidanku kece kika mallake
Habiba dole ba'a yi dole sai dake
Ruwan zuma Habiba
Ruwan rake Habiba
Written by: Ali Isah Jita
instagramSharePathic_arrow_out

Loading...