Credits
PERFORMING ARTISTS
Saadou Bori
Performer
COMPOSITION & LYRICS
Saadou Bori
Composer
Lyrics
[Intro]
Kai bori ya koma ga yara
Kai bori ya koma ga yara
Ya bar manyan mutane
Yara ƙanana ma su yi bori
[Verse 1]
E! Auta Jan Maye suka tsoro
Kai maye ɗan mayya suka tsoro
E! in Iya ta kama ya ka ceto
Auta ya kama ba a ceto
Kai mace kucaka ba ta bori
Kai mace ƙazama ba ta bori
E! kai wani kyawo sai ga bori
Kai wasu kaya sai ga bori
Iya bori abin hwa tsoro
Aljani abin hwa tsoro
E! Auta Jan Maye nika tsoro
Kai maye ɗan mayya nika tsoro
Haba! maye
[Verse 2]
Kai bori manyan sarakai
Yara ƙanana ba su yi nai
Ali abokina na da bori
Kai Jallo abokina na da bori
E! Manu abokina na da bori
E! ni na sa kaina a bori
E! Auta Jan Maye nika tsoro
Kai maye ɗan mayya nika tsoro
Haba! maye
[Verse 3]
ʼYan borin gıda da borin daji
Bori ko gıda shi na ishe dole
Idan mutuwa maza da tsoron soja
Mutuwa ko gida tana ishe ƙato
Ina ce soji birgimar hankaka
Soja wuta gudu barewar daji
Ina ce hattara kumandan mugu
Shillo ba shi kada ɗan Jemage
[Verse 4]
Don Allah maza ku ɗauki sarushe
Mutuwa ko gida tana ishe ƙato
Wani ya sha wuta kamar bai sha ba
[Verse 5]
E! wani ya sha wuta jiki ya sale
Written by: Saadou Bori

