album cover
Labari
455
R&B/Soul
Labari was released on June 5, 2026 by S.N.Y RECORD LABEL as a part of the album Labari - EP
album cover
Release DateJune 5, 2026
LabelS.N.Y RECORD LABEL
Melodicness
Acousticness
Valence
Danceability
Energy
BPM

Credits

PERFORMING ARTISTS
Garzali Miko
Garzali Miko
Performer
COMPOSITION & LYRICS
Garzali Miko
Garzali Miko
Songwriter

Lyrics

Su, Sultan with the beat baby
Ku taho da labari, ku taho da labari
Ku fito da labari
Ku fito da labarin daya sosa raina
Ku fito da labarin daya sosa raina
Ya saka nake kunci sanadi na kauna
Shiyasaka nakeyin kwalla a cikin idona
Gaskiyar batu nidai so yayi mini barna
Na tabbata reshe shike dab da ganda
Zakin rake shike yin yanayin takanda
So ruwan zuma ne amma ni yayi mini kwada
Kamar da wasa ya shige ni yanata tsanda
Kamar da wasa ya shige ni yanata tsanda
Ko an kira ma bana ji na toshe kunne
Kowa ki jin bari zayaji hoho ashe hakan ne
Hidima nake tayi mata kama da zubin adashi
Dashin daba ranar dauka wahala da koshi
Kuma zuciyata tanata gaya mini nayi goshi
Matsala ta so kunsa shi yana wahalar da mai shi
Tamkar gyada haka so ya sakani zama akonso
Bege da kewa nake a cikin rai yayi naso
Ya mamaye duk jiki yayi min wanka da soso
Bana gudun ko'ina in nuna wa nake so
So zai kashe ni
So zai kashe ni
Wayyo ni wayyo Allah wayyo ni wayyo
Wayyo ni wayyo Allah so zai kashe ni kece
Indai akwai rai ina nazari zanyo tinani
Zan gane mai sona da wanda yake kula ni
Kasanka abunka da yaro mai karamin tinani
Kajeka zan duba alkawarin mu idan yana nan
Na fadawa baba idan ya gamsu jirani sanan
Sai na fadawa mama kasan itace shirina
Bazamu maimaita rayuwar da mukai ta yara
Ai yin haka kuskure ne kasan lamari na kara
Ba boye-boye kai kasan aure nake so
In dai kana so toh mai zaya hana ni inso
Allah yana nan kuma shi yasan nufina
A batu na kaunarka ko a ina ban boye kaina
Ka zamo mijina inka yarda da zantukana
Amman batun soyayyar titti babu wanan
Ban yaudara ni kadaina fadin zan yaudareka
Bani yaudararka
Bani yaudararka
Bani yaudararka kasani ban yaudararka malan
Written by: Garzali Miko
instagramSharePathic_arrow_out􀆄 copy􀐅􀋲

Loading...