album cover

Habib

6,100World2018
album cover
Habib was released on July 6, 2018 by Apple Media Africa as a part of the album Tribal Grooves, Vol. 26
ReleasedJuly 6, 2018
LabelApple Media Africa
BPM84
Melodicness
Acousticness
Valence
Danceability
Energy

Lyrics

Taho, oh
Taho
A'ah, lala, lalala, haah
Tausaya wa rai na
A rayuwa zana so a ce kin barni
Ko domin kawar ki
Tayi halacci a rayuwa
Ita zuciya, duk mai kyautata mata dole ta so shi
Gare ni babu laifi, in naso ka zamo miji na
Na yarda dake, matsayi na aminiya na baki
Yau kin ci amana kin cuce ni a rayuwa
Indai da gaskiya son da kike mini so ne na hakika
Komai idan naso za kiyi mini ba batun shakka
Farin ciki na raina, zaki samar mini ko ruwa ko iska
Ina ma zaki barni, zana so ki a yar'uwa ta
Yaya kake barin wannan zance ya fito bakin ka
Kowacce mace tayi tarayya da kai bata barin ka
Don kyawawan hali wanda su suka zama jari gun ka
Yaushe zai cika burina, aure da kai?
Mai zan gani haka, gaske ne koko dai mafarki nake
Wannan cin amanar ni misalin shi kamar ya yake?
Na kasa gane komai yanzu zuciya sai kuna take
Dan Adam butulu, ni nama daina tantama
Sara kawai kike, bakin gatarin ki bakya dubi
Mata ta kawar ki ce, a gare ki kullum ta nuno hubbi
Ta kyautata miki, alkhairi dashi zaki maye mata gurbi
Rufa min asiri, taimake ni a rayuwa ta
Niko a duniya, in akwai wacce na tsana ita ce
Ta dauke hankalin ka, in na biyo hanya ta saka ka kauce
Wallahi ban barin ka, komai wahala nina nace
Kayi min dashe a zuciya da baya faduwa
Wayyo ni duniya, sai ka so mutum shiko bai kaunar ka
Nayi miki rana, kinyi min dare kaya kin sa na taka
Wannan shine sakayyar da zaki yi min kin saka nayi kuka
Nayi dana sanin dauwa ta dani dake
Written by: Umar M Sharif

Shazam Footer

Select language:
Google Play Store
Apple App Store
Chrome Web Store
Galaxy Store

Follow Us

Loading...