Music Video

Music Video

Credits

Lyrics

Ke nagani-nagani
A ina kagani-kagani?
Yanzu-yanzu
Yanzu zani baki labari
In na kulle ido na (um)
Ko na bude na (hnm-um)
Na baka zo ka amshi dukka soyayya
Naji anata fadi
Namiji kanin ajali
Ni ko nace, zancen su ba na gaske bane
Ni koh ganin da nayi
Kuskure kadan sukayi
Wacce ba tayi dace ba dole ta furta haka
Haduwar mu ni dake
Silar ta soyayya ce
Na dade ina nema
Na samo ba rance
Wanda ya so, in aka so shi
Yayi babbar nasara ce
Tunda kin so ni da gaske nima bani barin ki
Nagode miki zuciyata
Kin man adalci
Da kika sani na yarda da so mai inganci
So guda daya wanda babu hadi kuma ga yanci
Na tabbata gamon da nai da alkhairi
Naji anata fadi
Namiji kanin ajali
Ni ko nace, zancen su ba na gaske bane
Naji anata fadi
Namiji kanin ajali
Ni ko nace, zancen su ba na gaske bane
Ni koh ganin nayi
Kuskure kadan sukayi
Wacce batayi dace ba dole ta furta haka
Bana gajiya da jin zancen ki
Kar ki bari
Koh bacin rai
In na tuno ki sai ya sani fari
Cikin rayuwata kin zamo min tamkar gishiri
In babu ke, sai shiru
Don babu labari
Tarbiyyar da kayi mani kar ka canza halin ka
Tunda ka sani zuciya da ruhi na baka
Bani da buri da ya zarce in ga hakoran ka
Ma'ana farinciki in ganka da annuri
Naji anata fadi
Namiji kanin ajali
Ni ko nace, zancen su ba na gaske bane
Ni koh ganin da nayi
Kuskure kadan sukayi
Wacce batayi dace ba dole ta furta haka
Written by: Umar M Shareef
instagramSharePathic_arrow_out

Loading...