Music Video

Music Video

Credits

PERFORMING ARTISTS
Nura M. Inuwa
Nura M. Inuwa
Performer
COMPOSITION & LYRICS
Nura M. Inuwa
Nura M. Inuwa
Songwriter

Lyrics

Eh dawo masoyi na, kaiman irin rukon nan na al-'kawari
Duniya dadi na tabbata hakan inda rai da rabo
Eh garin masoyi, bai nisa 'kauna aran da jiki
Duniya dadi, mai gaskiya a rai baya 'badda kama
Eh nifa zance na baya wuce na soyayya (al-'kawari)
Na tsaya gunka na kyale masu yin 'karya (al-'kawari)
Da naji motsinka kunya ta sani nai 'buya (al-'kawari)
Nayi ma'anoni, ka fahimta so nike muyo sabo
Garin masoyi, bai nisa 'kauna arai da jiki
Duniya dadi, mai gaskiya a rai baya 'badda kama
Eh ina ka dosa tafiya bakayi waige ba (al-'kawari)
Rashinka guna a jiki bazan ji dadi ba (al-'kawari)
Kaizan fito nema a gari badan iyaye ba (al-'kawari)
Bzan amince ba zuciyata kai kadai takewa yabo
Garin masoyi, bai nisa 'kauna arai da jiki
Duniya dadi, na tabbata hakan inda rai da rabo
Eh da jin hakan to kin sakaleshi kin rike danye (al-'kawari)
Domin idanuna sanadinki sunyi jurwaye (al-'kawari)
Tuno da cen baya mu rike furen mu koraye (al-'kawari)
Mu samu 'yan yara da Hassan da Hussaini na ukun su ne Gambo
Dawo masoyina kaiman irin rukon nan n al-'kawari
Duniya dadi, na tabbata hakan inda rai da rabo
Garin masoyi, bai nisa inda 'kauna arai da jiki
Duniya dadi, mai gaskiya a rai baya 'badda kama
Eh ashe mafarkina watarana zai zamo gaskiya (al-'kawari)
Ciwon dake damun zuciya tawu zai warke (al-'kawari)
Albishir zan ma goro kabani nan take (al-'kawari)
Bazan fada ma ba komai kabani inaso banda kabo
Garin masoyi bai nisa inda 'kauna arai da jiki
Duniya dadi, na tabbata hakan inda rai da rabo
Eh farincikina daman kizama sha kallo (al-'kawari)
Wurin 'kawaye ki wuce a daina yin gwalo (al-'kawari)
Adinga nunaki ke zara ce da kin 'bullo (al-'kawari)
Dama yawan gashi kan zakara akwai babu kan Zabo
Dawo masoyin kaiman irin rukon nan n al-'kawari
Duniya dadi, na tabbata hakan inda rai da rabo
Garin masoyi, bai nisa 'kauna aran da jiki
Duniya dadi, mai gaskiya a rai baya 'badda kama
Duniya dadi, na tabbata hakan inda rai da rabo
Duniya dadi, mai gaskiya a rai baya 'badda kama
Written by: Nura M. Inuwa
instagramSharePathic_arrow_out

Loading...