制作

歌词

Mai hakuri karda ka daina
Kai ke tare da rabba
Kazama mai zurfin nazari
A sannu zakaci riba
Mai hakuri karda ka daina
Kana tare da rabba
Kazama mai zurfin nazari
A sannu zakaci riba
Mai hakuri karda ka daina
Kake tare da rabba
Kazamo mai zurfin nazari
A sannu zakaci riba
Rabbi nake sawa fari
Sarkin da shi yayi ni
Sarkin sarakai shine dai
Allahu ya rabbani
Duk inda zanje in na fadi
Shi zayayi mini tsani
Dogaro dakai kadai nayo Allah
Dafa mun in zamo babba
Allah ka kara salati
Gun رَسُولُ na mai girma
Wanan daka baiwa kur'ani
Ya issar gurin al'umma
Akan hakan yayi gwagwarmaya
Manzon mu yasha fama
Yayai juriya a cikin hakuri
Gashi muna cin riba
Mun zo a yau zamuyi waka
Hakuri muka dauko
Bayan dogon nazari
Muka gane shine farko
Komai in zakai sai in
Akwai shi zakayi karko
Ka tsarkake zuciya kaji dan uwa
Mahasada bazasu cimma ba
Allahu shine ya fadi
Cikin kur'ani mai girma
إِنَّ اللّهَ مَعَ الصَّابِرِينَ
Gurare naji su da dama
Wanda ya dauka ya dace
Yan uwa ku gwada kuma
A sannu zakuga riba
Wanda yayi ma abin sharri
Karka bishi da sharri
Kai kuma yi masa alkairi
Sai ka kai labari
In ka zamto cikin hakan
Shaida ayi maka tari
Koda husama ce ta hada
Ko bazaka zam rasa shaida ba
Haka zalika gun aiki
Wallahi sai ka jure
Idan kana son kazamo
Daban cikin su ka jure
Nayi gumi wayyo Allah
Wasu sun kace "na zare"
Amma hakan bai sa gajiya ba
Ko ace mun sare
Manyan mu su suka zam jigo
Garemu sunyo daure
Su suka ce mana sannu a sannu
Zamu zama a sahun gaba
Written by: Abdull D
instagramSharePathic_arrow_out

Loading...