歌词
Wasika yau zan ambata ta
Sako ne ga masoyiya ta
Kin dade a cikin zuciya ta
Na rasa yadda zanyi har ki fahimta
Tun farkon haduwar mu dake
Soyayya na kamu dake
Nauyin baki shiya hana ni inzo
Tunani kullum babu sake
Hawaye nayi ido ya jike
Kowanni sa'i sai kin min gizo
Yazam cuta gare ni kin gani
Kece kadai kawai magani
Tallafa kiyo lamuni
Ki bani son ki in shigo gari
Banjin dadin labari
In ba naki ba ba tsari
Ai ko a cikin taurari kinyi daban
Yardar ki nake yin buri
Ki aminta dani ba sharri
Nazo da dubun alkhairi son ki kiban
Ina ta sumbatu
Har ance na zautu
Bana iya karatu
Kece (kece)
Kece (kece)
Kece kadai magani na
Kyakkyawa mai kawata kallo kece
In kira ki da dawisu ado haka ya dace
A dabi'u koda gani ke mai natsuwa ce
In kin shiga taro ke tamkar fitila ce
Tauraruwa ta bullo
Da kin fito sai kallo
Ko za'ayi mini gwalo
Ko an kira ni da dolo
Ni ke kadai nayi kallo
Ko an buge ni da kwallo
Ban kauda kai ko zillo
Don kyan ganin ki da kallo
Kece (kece)
Kece (kece)
Kece kadai magani na
Written by: Umar M Shareef