歌词
Auta Waziri kuke ji uhm! ah ah
Farin cikinki shi ne farin ciki na ah
Ki bar gudu na ba inda za ni zauna
Uhm! Farin cikinka shi ne farin ciki na
Ka bar gudu na ba inda za ni zauna
Kina taɓa ni kina yawan tsuma ni eh
Ina kike ne kawai kira ni za ni
Abar faɗi na ke ce kawai a raina ah
Kin sanya ƙauna tana yawan zuga ni
Ki ba ni dama kawai ki ba ni soyayya
Mu sanya yarda ba a yi mana rauni
A kanki ne ma suke ta nuna ƙi suka
Baya gabana ina ta nuna soyayya
Farin cikinka shi ne farin cikina
Ka bar gudu na ba inda za ni zauna
Farin cikinki shi ne farin cikina
Ki bar gudu na, ba in da za na zauna
Idan da hali kar ka bar ni ɗan arziƙi
Ka zo mu zauna kai kaɗai na ba lokaci
Ina da dama da zana so su ma sai na ƙi
Suna ta bi na na ƙi yanzu sai tsokaci
Kawai ka gano kar wata rana ka je biki
Saboda mata ko ɗan abinci ma kar ka ci
Ina da kishi a kanka shi yasa za na ƙi
<span begin="1:38.098" end="1:42.024">Awa guda cir, idaniya ba sa gan ka ba</span> <span ttm:role="x-bg"><span begin="1:42.024" end="1:43.923">(Ba zan iya ba ah)</span></span>
Farin cikinki shi ne farin cikina
Ki bar gudu na, ba inda za ni zauna
Ni sonki ki ya kai munzalin da ban son faɗa
Ko na faɗa ma ba za a gane ƙarshensa ba
Ki gane cewa a sonki ni ko ban fargaba
Ba zan iya ba da wata in ba zan gan ki ba
Jinin jiki na da na ki sun haɗe gu guda
Wa zai raba su cikin ƙasar ga ban gan shi ba
A kanki za ni duniyar da ba namu ba
In dai kina nan na sani ba zan bar su ba
Farin cikinka shi ne farin ciki na
Ka bar gudu na ba inda za ni zauna
Farin cikinki shi ne farin ciki na
Ki bar gudu na ba inda za ni zauna
Kai ne a dama na, ba za ka kauce ba
Waninka ko ya zo ba za mu saba ba
Ka san da soyayya sai an yi haƙuri ma
Zama na rayuwa ma ya ba za a saɓa ba
Zan samu nutsuwa in kana zama guri na
Farin ciki ya kan zo ya ba zana gode ba
Kawai ka yarda Rabbi ya haɗa ni da kai
A lamurra na zan so a ce ka zamto gaba
Farin cikinki shi ne farin ciki na
Ki bar gudu na ba inda za ni zauna
Farin cikinka shi ne farin cikina
Ka bar guduna ba inda za ni zauna
Written by: Auta Waziri


