制作

歌词

[Intro]
Cikin raina
Na sanyo ki
Ki ba ni guri ke ma in shigo naki
Cikin raina
Na sanyo ka
Ka ba ni guri kai ma in shigo naka
[Verse 1]
Kamar wasa na yo dubi kamar gaske
Da so kin dasa cikin raina ya babbake
Filin zuciyata ko ta ina ke ce fake
Ba sauran gurin da za a shigo da ko keke
Na yo aike
Karɓa ki riƙe
Ban so ki sake
Soyayya ta ʼyar baba
[Verse 2]
Kallon ka idan na yo da ido nishaɗina
Ba sai na faɗi ba kai ka zamo muradina
Hannu ba zai iya goge abinda ke raina
Idan zai kwatanta hakan to babu motsina
Karatuna
Cikin kaina
Inda za a auna kai ne kake yin girma
[Verse 3]
Gani da ido shi ne shaida ƙwaƙƙwara
Ki je ki faɗi soyayyarki ba ni da tsara
Ina da shiri ko waye za na yo tinkara
Ya zo mu buga ni zan sa shi yay yo ƙara
Ba almara
Nake nasara
Ni ba na jira gun Allah nake yin nema
Cikin raina
Na sanyo ka
Ka bani guri kaima in shigo naka
[Verse 4]
Cikin raina
Na sanyo kI
Ki bani guri kema in shigo naki
Na buɗe ido na farka a barcina
Ga wanda nake so shi ne a damana
Ba na gajiya kai na riƙe madubina
In zan yi kiran ka da Larabci "Habibina"
Kana raina
Tarko na ɗana
Da kai na gina
Soyayya nake yin nema
[Verse 5]
Kai ne zakarana kai zan ba kanbu
Murnar haka zan ɗauke ki mu je lambu
Ba abin da nake sha'awa yau sai dambu
Domin ki a yau zan buɗe dukan rumbu
Sanin gaibu
Ai sai Rabbu
Ai ba aibu
Neman aurenki na ɗaɗa himma
[Outro]
Cikin raina
Na sanyo ka
Ki ba ni guri kema in shigo naki
Written by: Umar M Shareef
instagramSharePathic_arrow_out

Loading...