制作

出演艺人
Ali Jita
Ali Jita
表演者
作曲和作词
Ali Jita
Ali Jita
词曲作者

歌词

Mu gai da Salma, Salamatu gimbiya sarauta autar mata
Gai da Salma, uhm, sannunki Salma
Salam alaikum, Salamatu kin ji dan bayani
Ina da zance, amsa za na so ku ba ni
Ina ya Salma, a mata kun ji nai bayani
Kiɗa da busa ga Jita na sauya launi
Mu gai da Salma mai darajar da nai yaƙini
Ku tashi mata ku yi ta rawa cikin sukuni
Cikar gari ne in a garin ana da Salma
Salma gimbiya ce, mu mun santa mumina ce
Salma jaruma ce, mai nasara da arziƙi ce
Salma ʼyar gida ce komai ta yi shi ya dace
Sannunki Salma, kyan halinki ne ya yi ki
Sannunki Salma kin dace da arzikinki
A ba wa Salma mota ko a bata doki
Sannunki Salma sai faraʼa da ʼyan uwanki
Allahu Rabbi gatan Salma
Ɗiyar sarakuna ce Salma
Ɗiya ta maluma ceSalma
Farin jini yana gun Salma
Ado na gaske na gun Salma
Shiga kala kala sai Salma
Ina ta godiya Salma
Dubu-dubun ƙawaye Salma
Dubu-dubun masoya Salma
Dubu-dubun kuɗi sai Salma
Dala-dala a hannun Salma
Ku tafa hannuwa ga Salma
Ku dinga jinjinawa Salma
Ina irinta mata Salma
Tafiya irin ta mata Salma
Halin kwarai da kyauta Salma
Mahassada ku kyale Salma
Sai dai ilahu lamarin Salma
Gari gari ana jin Salma
Gida gida ana son Salma
Alfahari ta mata Salma
Alfaharin mazanma Salma
Take na Salma ne da salama
Nasara ta zam cikin alʼumma
Dama gare ta sai ta dama
Mu gai da Salma, Salamatu gimbiya sarauta autar mata
Written by: Ali Isah Jita
instagramSharePathic_arrow_out

Loading...