歌词
Auta Waziri kuke ji mallam
Na yarda da kai ne
(Beat Ali's Production)
Na yarda dake
Nasan kin yarda dani ma
Kar kiyi zaton zana guje ko nayi budurwa
Na yarda da kai
Nasan ka yarda dani ma
Bana da zaton zaka guje ko kayi budurwa
Kece ra'ayi na
Kuma ni kece a gaba na
Tsarin dana dauko kullum inji ya kika kwana
Bana da bukatar inga an sanya ki a rana
Kece a mafarki kike gyaran bacci na
Wai ya hakane?
Wasu sun ce ba haka nan ba
Nikam na fada, nace masu sone bai wuce nan ba
Na yarda da kai
Nasan ka yarda dani ma
Bana da zaton zaka guje ko kayi budurwa
Na kosa na fada, ni kaine mafadi na
Mai chanzan ra'ayi, ko basa so suji batu na
Tauraron masana, bana so aji muyi bankwana
Zanyo alfahari, ni a gidan ka nake son kwana
Ban boye maka ba
Kuma baza nayi maka karya ba
Kalmar mara da ni baza tayi mini komai ba
Na yarda dake
Nasan kin yarda dani ma
Kar kiyi zaton zana guje ko nayi budurwa
Soyayyar dana dauko, tana haskan kirji na
Ni yar dana samo, tana sharan kuka na
Ko kun ga baki na, ita ko sai taga fari na
Bata da makusa, abar so tayi mini rana
Wai ya akayi?
Bana sai sauyin yanayi
Kwarya tabi kwarya
Nikam kece ra'ayi na
Na yarda da kai
Nasan ka yarda dani ma
Bana da zaton zaka guje ko kayi budurwa
Ni nasa ka a ruhi na
Kuma zan nuna ka gaban kowa
Kaine na gaban goshi na
In baka kusa nayi kewa
Matsala in ta afku ba wani mai iya debewa
In har ance ga ka sai inji ban rasa komai ba
Wai ya hakane?
Wasu sun ce ba haka nan ba
Nikam na fada nace masu so ne bai wuce nan ba
Na yarda dake
Nasan kin yarda dani ma
Kar kiyi zaton zana guje ko nayi budurwa
Na yarda da kai
Nasan ka yarda dani ma
Bana da zaton zaka guje ko kayi budurwa
(Ali's mix)
Written by: Auta Waziri