音乐视频

音乐视频

制作

出演艺人
Namenj
Namenj
表演者
作曲和作词
Emmanuel Reuben
Emmanuel Reuben
作曲
Ali Jubril Namanjo
Ali Jubril Namanjo
作曲
制作和工程
Mega Mix
Mega Mix
制作人

歌词

Ali Namenj
Sun yi sun yi su raba, Allah bai yi ba
Auren da Allah Ya haɗa ba mai rabawa
Rabonka ba ya wuce ka, ko yana bakin kura
Allah shi ne ya haɗa ba wani ba
Soyayya ce, lobayya ce
Fahimta ce, ke sa zauna lafiya
So da ƙauna, ku so juna
Hirar ƙauna zai sa mu dinga son juna
Amarya, rabonki ne
Kin zama matar mai sonki
Ango rabonka ne
Ka zama mijin mai sonka
Amarya, rabonki ne
Kin zama matar mai sonki
Ango rabonka ne
Ka zama mijin mai sonka
Mamar amarya wai ina kike ne
Ga ta nan, ga ta nan, Allah sa albarka
Mamar ango wai ina kike ne
Ga ta nan, ga ta nan, Allah sa albarka
Mun gane wance da wance ba sa so
Tun da Allah yana so, kar su so
Ba wanda zai iya kwance ƙullin so
Wanda Allah ya haɗa wallahi babu sharri
Lokaci ya yi mun zo auren soyayya
Share hawayenki, amarya ki yi murna
Riƙe mijin naki soyayya ki nuna
Ka riƙe matarka, kulawa ka bata
Amarya, rabonki ne
Kin zama matar mai sonki
Ango rabonka ne
Ka zama mijin mai sonka
Amarya, rabonki ne
Kin zama matar mai sonki
Ango rabonka ne
Ka zama mijin mai sonka
Mamar amarya wai ina kike ne
Ga ta nan, ga ta nan, Allah sa albarka
Mamar ango wai ina kike ne
Ga ta nan, ga ta nan, Allah sa albarka
Mamar amarya wai ina kike ne
Ga ta nan, ga ta nan, Allah sa albarka
Mamar ango wai ina kike ne
Ga ta nan, ga ta nan, Allah sa albarka
Mu taka rawar ƙauna, ƙauna, ƙauna
Mu taka rawar murna, murna, murna
Mu taka rawar ƙauna, ƙauna, ƙauna
Taka rawar murna, murna, murna
Written by: Ali Jubril Namanjo, Emmanuel Reuben
instagramSharePathic_arrow_out

Loading...