Lyrics

So na ne fa, on the beat Shi so ruwan zuma kuma ruwan guba ne ban rasa ko daya ba Ya zanyi ne da so, na ga duniya kai kadai take duba Indai akwai lalura cikin jikina bai wuce kauna ba So yadda nayi nufi wata kila ba haka zaka zomin ba Tamkar ana kafi, in kama so bai san wata kara ba Zai kama zuciya ya bi jijiya ma bazai tsaya nan ba Ni dai masoyiya ta kece, jinin jikina Inna rasa ki to zan zauce, ji lafazi na Komai nake bida dan kece, dare da rana Ba'a ziga ni dan in barki, babu ruwa na So yayi gurin zama ya zauna, a zuciya na Ni bani son ki yada amana, mu rike juna Karki bari in shiga damuwa, tunda so nada hadari Ke nake ambato kawai, inna zauna wuri-wuri Ni dake munyi alkwar, baki sanya ni garari Naga duk martabar miya, bai wuce maggi-gishiri Dukka mai so akwai jarabta gareshi ko wanne lokaci Kaddarar so idan ta farma sai ayi ta cema mahaukaci Babu komai ga dukka mai yin so hakuri ne hakika ci Tunda ma duniyar ta Allah zamanta bama da tabbaci Kai kana son wani yana son ka kaji so mai kulafuci Kara rudi na zuciya ya zuga mu fita hayyaci So akwai damuwa kunji yan uwa na Yadda Allah yaso haka zayayi min Ahh, nagode
Writer(s): Sani Ahmad Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out