Music Video

Music Video

Credits

COMPOSITION & LYRICS
hamisu said yusuf
hamisu said yusuf
Songwriter

Lyrics

[Intro]
Prince Production
[Verse 1]
Burin zuciya
Haɗa da idaniya
Su sami ganinka ya
Mai saka na yi dariya
[Verse 2]
Muradin duniya
Sonka har yai lubiya
Ka san duka zuciyata
Na bar maka taka ce
[Verse 3]
Duka yabonki da ni kike
Kuma sakan nutsuwa yake
In ina da rabo, sanadinki zan yi sake
[Verse 4]
Ban da ke wa zan riƙe
Kin sani ƙauna nake
Sai ki sa yarda, ni da ke muka yi dace
[Verse 5]
Kai nake so (Na sani)
Ka ga dafin so (Na gani)
Tunda ka kalla me kake jira (Ki yi min tuni)
[Verse 6]
So nake ka zamo miji
A garen ka yi agaji
Ka ga ba wani jan aji
Na sani ka san dai a kanka ban ji ban gani
[Verse 7]
Ni ma ban ji ban gani
Taimaka ki tsaya mini
Tun da kin fama minni zuciya ciwo take mini
[Verse 8]
Kin rufa saya mini
Kin ga je ɓoye mini
Sirrikan da na ba ki tunda ba ki min wauta
[Verse 9]
Ka ga komai za a bayar
Don ya zama fansa maɓoyar
Sonka ba zan ambata ba
Da ace so zahiri ne, sai ya zo mana baɗini ne ni abin da nake wa duba
[Verse 10]
Na ji zance naki daidai
Da na cikin rai nawa sai dai
Ni ba zai yiwu na ambata ba
[Verse 11]
Zan kira ki masoyiya
Ko in ce zinariya
Ki zamanna idaniyata, ko me ye ke za ki hango
[Outro]
(Midget Mix) Ka zamanna idon gani na, ko me ye kai za ka hango
Written by: Hamisu Breaker, hamisu said yusuf
instagramSharePathic_arrow_out

Loading...