Lyrics
Kudiri zancen zuciya ta
Alkhairi ne zo kiji
Aure dake zani so mu kulla
Kudiri zancen zuciya ta
Alkhairi ne zo ka ji
Aure da kai zani so mu kulla
Duniya kowa da kudirin sa
Anfi son mai alkhairi
(Ahh-ahh-ahh)
Ni dake hanyar mu daya ce
Bamu bin mai sharri
(Ahh-ahh-ahh)
Raya sunnar manzo ma'aiki munka dauka buri
(Ahh-ahh-ahh)
A sannu zaya cika a daure
Kudiri zancen zuciya ta
Alkhairi ne zo ka ji
Aure da ke zani so mu kulla
Wanda ya rike gaskiya
A rayuwa za ayi masa shaida
(Ahh-ahh-ahh)
Ko cikin al'umma bayani dole shi za a tsaida
(Ahh-ahh-ahh)
Mai irin wanga hali ta ko'ina zaiyi wuya a kada
(Ahh-ahh-ahh)
Na samu nau gare ku gashi na nuna
Kudiri zancen zuciya ta
Alkhairi ne zo kiji
Aure da kai zani so mu kulla
Kudiri zancen zuciya ta
Alkhairi ne zo ka ji
Aure da kai zani so mu kulla
Tafiya ni da ke zo mu jera
Ban wuce ki koda a sahara
Ba a nunawa kurege dabara
Takun mu ni dake dole a sara
Kalaman ki zo ki min in saurara
Don in na tuna koda yaushe na dara
Menene kunci? In akwai ki bansan shi ba
Kudiri zancen zuciya ta
Alkhairi ne zo ka ji
Aure da ke zani so mu kulla
Tausayi dole ne
Gashi kai kazame mini garkuwa
A rishin ka wajibi in shiga damuwa
Har idanu suyi ta zubar ruwa
Bani so inji kalmar rabo
Ita ke sanya rai ya shiga damuwa
Dani da kai sai dai ta Allah
Kudiri zancen zuciya ta
Alkhairi ne zo kiji
Aure da kai zani so mu kulla
Written by: Umar M Shareef


