album cover
Sama
5,406
Worldwide
Sama was released on July 6, 2018 by Blue Pie Records USA as a part of the album Tribal Grooves, Vol. 44
album cover
Release DateJuly 6, 2018
LabelBlue Pie Records USA
Melodicness
Acousticness
Valence
Danceability
Energy
BPM173

Credits

PERFORMING ARTISTS
Yakubu Muhammad
Yakubu Muhammad
Performer
COMPOSITION & LYRICS
Yakubu Muhammad
Yakubu Muhammad
Composer

Lyrics

Eh mai sama Allah, begen da nake na samu
Nai sama shillo aure igiya na kamo
Nayi ziyara gun wanda nake san aure
Nayi dubara, yau na zama matar aure
Eh mai sama Jallah soyayya yau ta 'bullo
Zan sama lilo aure a 'kasa na tono
Zo da bu'kata ke haddasa 'daurin aure
So da aminci sun sanya munyo aure
Mai sama Allah, begen da mukai mun samo
Muyi sama shillo aure igiya mun kamo
Munyi ziyara, ga wayanda muke san aure
Munyi dubara yau mun zama matan aure
Eh wheelbarrow ya 'debi icce dan gata
Nida yaro anyo mana auren gata
Wasu sunce zaki baya rabar gauta
Nayi murna nai aure ina 'yan mata
Mai sama Allah, begen da mukai mun samo
Muyi sama shillo aure igiya mun kamo
Munyi ziyara, ga wayanda muke san aure
Munyi dubara yau mun zama matan aure
Shazimami auren mu daku 'yan mata
Sunna ce mai 'karfi na baban binta
Sanki zobe ya zagaye duk manufata
Yau bikin mu wallayo nai rata
Mai sama Allah, begen da mukai mun samo
Muyi sama shillo aure igiya mun kamo
Munyi ziyara, ga wayanda muke san aure
Munyi dubara yau mun zama matan aure
Aure mukai dan so da amincin juna
Zuciya ce ke pallasa sirrin juna
Yo kalamin so, domin ya hanan kuka na
'Kamshinka ya 'kawata lumfashi na
Eh mai sama Jallah soyayya yau ta 'bullo
Zan sama lilo aure a 'kasa na tono
Zo da bu'kata ke haddasa 'daurin aure
Eh mai sama Jallah soyayya yau ta 'bullo
Zan sama lilo aure a 'kasa na tono
Zo da bu'kata ke haddasa 'daurin aure
So da aminci sun sanya munyo aure
Zuciyar soyayya in ta zamo garwashi
Zan kiraki domin kiyo rarrashi
Mai bukata duk rintsi baijin haushi
Shaki murhu zan jefa turaren 'kamshi
Mai sama Allah, begen da mukai mun samo
Muyi sama shillo aure igiya mun kamo
Munyi ziyara, ga wayanda muke san aure
Munyi dubara yau mun zama matan aure
Ke 'kawa taho taso da gudu 'yan gata
In na rausaya ko ba hanci kayi guda
Yaka gadali wallahi Allah kazama 'da
Kazamo gwani, sassan raina ka kurda
Written by: Yakubu Muhammad
instagramSharePathic_arrow_out􀆄 copy􀐅􀋲

Loading...