Lyrics

Soyayya bazan kara ba Sai watarana, kayi uzuri guna Nayi a baya ban ji da dadi ba Soyayya, ta mamaye rai na Kiyi dubawa, tallafi ruhi na Sai watarana, kar kiyi furtawa Wanda nake so a gida ance ba shi ba Mun so juna, yau mun rabu ba son rai ba Ya zanyi da rai na? Ido na hawaye duba Soyayya bazan kara ba Sai watarana, kayi uzuri guna Ki share hawaye Kuncin zuciya zan yaye Zanyi biyayya, gun iyayen ki ban tawaye Abin da suke so, zanyi shi ko dayan zan kiyaye Soyayya ta kiyi karbawa Sai watarana, ban so kiyi furtawa Nayi ritaya, kakin so ban sanya wa Halin samari, sun nunan ban mantawa Na yarje mai, ni yayi shirin cutarwa Dakin so, ciki ban komawa Sai watarana, kayi uzuri gu na Allah masani ne, niyya ta inyi auren ki Ki yarda dani, in share hawayen idon ki Kiyi imani, da Allah zai taimake Shi aure, sunnar manzo ne In har kin ki kinyi mai tawaye Zan baka amana ta, sai kayi karbawa Ka soni don Allah, kar kayi cutarwa Kishin dake ciki na, ka zamo mai bani ruwa Nayi alkawar, bazan saba ba Amanar ki bazan cinye ba
Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out