Credits
COMPOSITION & LYRICS
Hairat Abdullahi
Songwriter
Lyrics
Idan da rai
Idan da rai da rabonka duniya tabbas mai hakuri
Watarana tabbas zai dacewa
Kuruciyar ma ta kai ga an girma fitar rabo
Kamar misalin hadarin ruwan sama wata da zai zubo
Shi arziki samo irinshi alkhairi, dukkanin bawa Rabbi ya sakawa
Idan da rai da rabonka duniya tabbas mai hakuri
Watarana zai dacewa
Sa'ar da ke zuwa a rayuwa hassada bata bin
Komai ka barwa Jallah khalikin kowa Ya Raheem
Dake, dake mai mo matattarar sirri zai ma rabo
Kai kuma kar ka kosawa
Idan da rai da rabonka duniya tabbas mai hakuri
Watarana zai dacewa
Da yekuwa cikin tausassar murya nake amo
A hankali mai hakuri cikin duniya yake zamo
Toh kar muki, karmu mu kyautato buri
Mu zam da kwarin gwiwa karda mu sarewa
Idan da rai da rabonka duniya tabbas mai hakuri
Watarana zai dacewa
Komai ama ka dauki duniya a sannu da cigaba
Mai hakuri bai faduwa da sakayya da jaraba
Shi lokaci gamu yana cikin tsari
Idan da rai, watarana za'a dacewa
Idan da rai da rabonka duniya tabbas mai hakuri
Watarana zai dacewa
In samu, in rasa, khairat zani godewa
In kwanta, in tashi ikon kane yake biyowa
Ka bani ka kara kullum ina ta godewa
Kana kara dadawa
Idan da rai da rabonka duniya tabbas mu hakuri
Watarana zai dacewa
Written by: Hairat Abdullahi