album cover
Labiba
1,974
R&B/Soul
Labiba was released on January 1, 2017 by Shareef Studios Invest Nig Ltd as a part of the album Babbar Yarinya
album cover
Release DateJanuary 1, 2017
LabelShareef Studios Invest Nig Ltd
Melodicness
Acousticness
Valence
Danceability
Energy
BPM89

Music Video

Music Video

Credits

Lyrics

Masha Allah
Labiba-Labiba-Labiba
Labiba-Labiba-Labiba
Amarya mun kawo angon ki Labiba yau ranar murna ce
Labiba ki godewa Allah don yau ya cika burin ki
Labiba-Labiba-Labiba
Hamdan kasiran bilLah sarki masanin sirri
Da ya bamu iko na ganin wannan ranar mai khairi
An daura aure na da Labiba yau na cika buri
Godiya nake maku abokai (abokai)
Kun nuna kishi ba son kai
Dama ace ina da dawakai
Da sai in maishe ku sarakai
Labiba-Labiba-Labiba
Ango na ka nuna son kai tunda ka manta kawaye
Sune suke tausa ni, in nayi kuka su share hawaye
Duk da dai farin ciki ne da zafi rabuwa da iyaye
Ya Allah ya barmu a tare
Kawaye na karda mu ware
Labiba-Labiba-Labiba
Ku bude kunni kuji shawara ce muke baku
Kuyi wa juna adalci a cikin zaman ku
Sannan kusan cewa hakuri ne farkon abin luran ku
Fatan mu rabbi yasa albarka kuga jikokin ku
Iya sanin mu Labiba tana da kyan hali kuma ga kunya
Muna da yakinin zatayi wa ango ladab da biyayya
Labiba mai hakuri ce kuma tayi dacen samun tarbiyya
Kyakkyawan zato mukayi miki don Allah karki bamu kunya
Komai yayi farko zaiyi karshe har ya zamo labari
Tunowa nake don ban mantawa haduwar mu na fari
A sanda muka faro soyayyah yau gashi mun cika buri
Mafarki nake yi ko gaske abin mamaki
Dani da zabin raina ne yau aka samu a daki
Matsayin ma'aurata sunnah babba gun shi ma'aiki
Muje muyi alola, sannan muyo sallah
Mu godewa Allah
Labiba (Labiba), Labiba (Labiba), Labiba (Labiba)
Written by: Umar M Shareef
instagramSharePathic_arrow_out􀆄 copy􀐅􀋲

Loading...