Credits
Lyrics
Nazari
Mu dinga nazari
Nazari
Mu dinga nazari
Kafin farawa gare ku sai nayi sallama
Abokai da yan'uwa ga hannuna ku kama
Nine naku M. Shareef dan karamin alaramma
Jariri a cikin mawaka ne watarana a sama
Ni nazo da yar nasiha ta gun al'ummah
Idan an maka sharri dan'uwa karda ka rama
Wanda yasha madaci yau gobe ka ganshi da zuma
Mai gona ta sharri shine zai girba nadama
Nazari
Mu dinga nazari
Nazari-nazari-nazari
In kaji ana yin zancen ka ai ka kai ayo ne
In ka dau wancan masoyi wani makiyi ne
Ka wuce ana ta zagi wasu kuma yabo ne
Nida na gane
Sai na toshe kunne
Kaima ka toshe naka bar hangen wane-wane
Abinda Allah yaso ka samu wajibi
Komai a hankali ne rayuwar mu tana tsare
Rabon ka bai wuce ka koda kana a zaune
Kukan kurciya jawabi ce inji mutane
Niko inda zanyi nawa a baituka ne
Kar ka fidda rai da samu in kana a raye
Kar ka fidda rai da samu in kana a raye
Nazari
Mu dinga nazari
Nazari-nazari-nazari
Duniya, duniya ce makaranta har da malami
Dauki takardanka ka karanta da alkalami
Kar da ka yarda ayi maka rata, dinga azumi
Kar ka biyewa zuciya ta saka ka zauce
Nema tsari ga Rabbi shaidan kanka kar ya dace
Addu'a ga mumini ta zama garkuwa ce
Allah sa mu dace
Zunubai mu kauce
Toh sai mu jajirce
Aiyuka mu nace
Nafi son in ganni a sahun farko
Mai yin murna da samun sakamako
Kyakkyawa da an kirani in miko
Dacewa gun Ilahu muyi nema ba danadam ba
Nazari
Mu dinga nazari
Nazari-nazari-nazari
Mu dinga nazari
Written by: Umar M Shareef