Music Video
Music Video
Credits
COMPOSITION & LYRICS
Abdullahi Mansur
Songwriter
PRODUCTION & ENGINEERING
SSG
Producer
Lyrics
Oga Abdul
White House Family
(Zango Boy)
Akwai batu
Ko'a jiki na don suna sa min ido
Masu gulma da zagina na dau hakan ado
Duk mai hankali yasan ruwa gatan bado
Sai a kara kara hakuri malam ciwon ido
Ko ka so ni dai
Ko ka zage ni dai
Na rantse baka taba canza min kaddara
Dara ga dare Allah ne yayi kadangare
In ina ci da waka wasu suna cewa sana'ar bara
Lollipop, nayi dope
In sipper ruwa na a cup
Baka bani ci, baka bani sha
Inda Magriba zan mutu baka sawa in kai Isha
Baka kera kai, kuma baka busa rai
Kaima kamar ni kake a ci, asha aje masai
Dani dakai duka muna laifuka
Watakila a bincika ka fini yawan shafuka
Yan sa ido, ku ringa sa ido (eh ku ringa sakamin ido)
Yan sa ido, ku ringa sa ido (magulmata gishirin zaman duniya)
Kana da, ina da
Ammah kake samin ido
Kina da, ina da
Mene na sakamin ido
Ka kama Rabbana ka kyale dan Adam
Wasu ko halal kake ci wani sai sun kira ta da haram
Suna nan a tare hadarin su yafi boom
Lokaci suke jira ka samu sai su maka gum
Da in zama dan sarki gwara in zauna lafiya
Na gaida magulmata gishirin zaman duniya
Allah raba ni da yan bani na iya
Masu rokon ruwa a cokali suna da maliya
Baka san ka ganni ina dariya
Baka san ka ganni cikin koshin lafiya
Toh ai kai ba Allah bane
Kaje ka bincika sunan mijin iya ai baba ne
Baka son ka ganni ina dariya
Baka son ka ganni cikin koshin lafiya
Toh ai kai ba Allah bane
Kaje ka bincika sunan mijin iya ai baba ne
Yan sa ido, ku ringa sa ido (eh ku ringa sakamin ido)
Yan sa ido, ku ringa sa ido (magulmata gishirin zaman duniya)
Kana da, ina da
Ammah kake samin ido
Kina da, ina da
Mene na sakamin ido
Oga Abdul
Kana da laifin ka ina da nawa
Kayi harkan ka inyi nawa
Ko'a jiki na
Written by: Abdullahi Mansur


