Music Video

Music Video

Lyrics

[Verse 1]
Gimbiya Aisha
Sarauniya ce Aisha
Aisha ki zo ki karbi kidan girma
Aisha kina da babbar alfarma
[Verse 2]
Indo Indo da Aisha
Eh Indo Indo da Aisha
Ga ta abokinmu Aisha
Sarauniya ce Aisha
Ga mai kwalliya ina Aisha
Ga mace ta gari taho Aisha
Mai sarauta Aisha
[Verse 3]
Ke kwanta cikin kilishi huta
Aisha zauna a miki fifita
Aisha zana so ganin angonta
Sarauniya ce gimbiya
[Verse 4]
Kyakkyawa ku tambaya
Mai hakuri ce farar diya
Mai nutsuwa ce 'yar hajiya
An kira ta zinariya
[Verse 5]
Aisha Aisha
Aisha Aisha
[Verse 6]
Aisha dole ne na dan yi miki take
Masu sarewa ku yi ta yi gobe da sake
Ai hakuri ba a fi ta ba
Kwalliya ba a fi ta ba
Ilimi ba su fi ta ba
Nutsuwa ba su fi ta ba
[Verse 7]
'Yar babban gida ce Aisha
'Yar manyan mutane Aisha
Kun yi kudi sarauta Aisha
Ga ilimi a familyn Aisha
Ga asali a familyn Aisha
Ga dangin yawa na su Aisha
[Verse 8]
Ga Indodo ga Indodo taka sannu
Ga Indodo ga Indodo taka sannu
[Verse 9]
Ga Indodo ga Indodo sarauniya
Gai da Abubakar masoyin Indo
Soyayya ku yi ta kwando-kwando
Ba tsoron mutum bare wani dodo
Ku yi wasa da ita gardo-gardo
[Verse 10]
Aisha Indo Indo
Aisha ce gimbiya
Aisha sarauniya
Aisha ce gimbiya
Aisha sarauniya
[Verse 11]
Mai tafiya a hankali
Mai magana a hankali
Ga idonta da tozali
Indodo mai tawakkali
[Verse 12]
Zana je na ga Aisha
Can gidansu Aisha
Aisha Aisha
[Verse 13]
Saka sarka ta gwal ki sanya turare
Don wankanki ya wuce na amare
Ai kyakkyawa ce Aisha
Walla ko an bincika
[Verse 14]
Ba za a samu kamarta ba
Aisha za ta haskaka
Cikin kawayenta tai gaba
Aisha mai halin uba
Ko rawanin bai guje ta ba
[Verse 15]
Sannu sannu Aisha
Sannu sannu Aisha
Sarauniya ce Aisha
Sanya alkyabba Aisha
Sanya zinare Aisha
Sanya takalma Aisha
Sa azurfarki Aisha
[Verse 16]
Dauki kwalbar zuma ki sha
Abubakar ne na Aisha
Yace in wake Aisha
Gimbiya ce Aisha
Sarauniya ce Aisha
AS na Aisha
Written by: Ali Isah Jita
instagramSharePathic_arrow_out

Loading...