Lyrics

Eh yeh kin bakanta mani Ta faranta mani Ga tsiya kin mani Ita ko arziki taimani Arayuwar da mukai nidai ina ganin na 'bata Itace tai cigiya danazo godiya nai mata Kin sani yin kuka, innai zance ki tanka Duk sanda na farka na tunoki sai inji ya haka Ita kyakkyawa ce Ana fadin na dace Abokanai sun tantance Asanta wai na nace Ga waya na rike kirata ko ina ma take Mu rayuwa babu ke Kuma nasan hakanan kike Son ki ni na soma Cikinsa babu nadama Zuciya kika kama Eh ke kinsani na suma Sanadin halinki ne shima Lokacin ina tayin rama Wasu ko suna tayin gulma Ina rasa gane kanki Kamar da iskokai kanki Ana fadin in 'kyaleki Ruwan ido ya cika gunki Duk da haka na soki Inata rokon sauki Gaskiya kika 'boye Akwai wanda kika sauye Hakki naso kin tauye Kin taba fada mini Da wasa kikai mani Shine kike yawan dai gani Zuciyarki ya shiga har jini Dukda ya yaudare ki Nikuwa na tallafe ki Gashi kin sani raki Kinki sauyo halinki Kina nan akan bakarki Maimakon ma 'kawarki Shawara ma ta baki Aurenki zaifi Dakintayin laifi Inganki kedashi zafi Dama wanine zaifi Ina tayin dogon hange Acen nasamo wata Bilki Tasani bana yin waige Ki hakuri in na mangareki Meyasa ma nasanki Babu hali in soki Akan kine wasu mutane Da zan wuce na kasa kunne Sunkace ni mayaudari ne A kofar gidan su A'i Bayan sallar Isha'i A shagon kawun su A'i Dan a hanani A'i To munyi sallah du'a'i Ciki ma munyo du'a'i Allah ya kauda 'yan bala'i Muyi aure da A'i Mu samu zuri'a da A'i Ke kuma na yafe maki Tsakanin mu babu hakki Allah ya nunan aurenki In figo kudi abaki Inba makiya mamaki Nine dan uwanki Kema zaki zoki Bikina da mijinki Yiriri zanyi murnaah
Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out