Credits

PERFORMING ARTISTS
Danmusa New Prince
Danmusa New Prince
Performer
COMPOSITION & LYRICS
Musa Muhammad Dan musa
Musa Muhammad Dan musa
Songwriter

Lyrics

Dan Musa yazo da waka
Waka-aa-aa-ah waka
Waka da salo ni ban ki na rera ba
In zayyana siffofin da kikai sama
Kafin in tafi ni zan bar sakon kauna
Kar kune yaji sa zuciyarki ta saurara
Zan so wata rana ki dan tina sashe na
Dan sako na waya bai kauda lalura ba
Murya naji ba in karanta kitabi ba
In na dawo in cika miki alkawarin bara
Kyakkyawa kyakkyawa
Kyakkyawar yarinya
Ga waka kita rawa nuna min kin iya
Ki mana girki lagwada sa mana naman miya
Ki mani shayi madara karda ki sa Bonvita
Yarinya dan tsaya
In bake sai rigiya
Dan in so ya shiga
Kisan na wahalar fita
Ga tsabta ga cika
Sanan kin iya alwala
Yau ga kyau na zuba
Mamanki ta iya haihuwa
Da kin mini wanan dama
So ya cika tsanza
Da nagaka fure mai 'ya'ya
Sai in tina ke ma
Idan akace bayki zo ba
Dole ido yayi kewa
Ganinki yasa inyi kuka
Ba irin na fushi ba
Kyakkyawa kyakkyawa
Kyakkyawar yarinya
Ga waka kita rawa nuna min kin iya
Ki mana girki lagwada sa mana naman miya
Ki mani shayi madara karda ki sa Bonvita
Written by: Musa Muhammad Dan musa
instagramSharePathic_arrow_out

Loading...