Credits
PERFORMING ARTISTS
Namenj
Performer
COMPOSITION & LYRICS
Ali Jubril Namanjo
Composer
PRODUCTION & ENGINEERING
Baba Ali
Producer
Lyrics
Namenj ne
Kuma naku ne
Ki tafi da ni, tafi da ni
Tafi da ni can-can
Ki tafi da ni, tafi da ni can
Birnin soyayya
Ki tafi da ni, tafi da ni
Tafi da ni can-can
Ki tafi da ni, tafi da ni can
Birnin soyayya
Alƙawarin soyayya ni na ba ki
Ja ni mu je yarinya zan biyo ki
Ga jirgin soyayya za na ɗauke ki
Maƙiya za su ji kunya in na aure ki
Ba ni fulawar ƙauna
Na ba ki chukui yarinya
Karɓi tukuicin raina
Mu rayu cikin soyayya
Ki tafi da ni, tafi da ni
Tafi da ni can-can
Ki tafi da ni, tafi da ni can
Birnin soyayya
Ki tafi da ni, tafi da ni
Tafi da ni can-can
Ki tafi da ni, tafi da ni can
Birnin so
A rayuwata ke za na baiwa gata
Bishiyata mai yaye damuwata
In babu ƙauna ba ke a rayuwata
Da ke na saba kin zamma garkuwata
Gani a nan, zo ki ta nan
Ki kau da kewata
Ke na riƙa, kar ki sakan
Kin kama kurwata
Ki kau maɗaci, ki ban zumar ƙauna
Ki tafi da ni, tafi da ni
Tafi da ni can-can
Ki tafi da ni, tafi da ni can
Birnin soyayya
Ki tafi da ni, tafi da ni
Tafi da ni can-can
Ki tafi da ni, tafi da ni can
Allah kawo rana da ni da ke mu yi aure
Tun da mun sasanta zamanmu to zai daure
Ki rayuwa da ni baby na gareki na zamto kyaure
Ai ni da ke ba kunya na zaɓi mu zauna tare
In da za ki je, ki ja ni mu je
Da ni da ke ba ware
Zan biyo nan, don mu tsallake
Dukkan wahala zan jure
Ki tafi da ni, tafi da ni
Tafi da ni can-can
Ki tafi da ni, tafi da ni can
Birnin soyayya
Ki tafi da ni, tafi da ni
Tafi da ni can-can
Ki tafi da ni, tafi da ni can
Birnin soyayya
Written by: Ali Jubril Namanjo

