Lyrics

Ahayye matan Arewa kun mai mata Allah tsare idanuwan ku ranar kallo Eh mana Eh ahayye matan Arewa kun mai mata Allah tsare idanuwan ku ranar kallo In dai har inda rato sarkin hattara Domin mai banbara ba bai yin tauna Ko an tinzira ba'a fin gaban hakura mun sani Dan hannu bayi kare hasken rana Su kara, kuda kar su kara suna gani Gwanja yau nazamo gutunbun bauna Bana kallon makiyi asara Domin sai da irinsu za'a kai jan kololuwa Mata kuji Gwanja be da dake Ku taso muci duniya da tsinke Mubar masu nawa suje su noke Ni dai nai damarar gudu da falke (toh) Idan nayi da kyau ku bani maki Ni mata na Arewa zan wa take Da karba, karba akanyi danga Idan kai daya kayi to da sake Ni da mata tafiyar mu naga ta dau haske Inda duk sun kayi za'a bi su bana yin makowa Ga zarena na dinka taguwa ta Duk dai nasan duniya dai da fadi Zamani yayi wa baka gata Bishi kar kai masa hassada da kaudi Lamarin Allah kuga wanda yaja To da rami a gaban sa zaya fadi Mai salo in kaji yayi karka tanka Nayi mata suka ce abin da dadi Mai kare kama karen ka tunda kura tazo Bani hanu baka kan na koshi in hau neman ruwa Ke kaza daina tone-tone karki tono mana abin duniya Da rana, da rana tsaka Ko a taro ba duniya idan har an zo Bayi kaiwa sai yan Arewa mata sun zo Ashe dai kaska tana da haushin kifi Shi ko girman dan saniya yakai yayai tozo Shi ko girma Allah ka baiwa kowa yaso Masanin darajar mata an kacewa gwarzo Ashe dai mu damunar tazo Muyi dua'i dan kar mu dinga kukan ansha ruwa Da haushi in guje a dawo mini Da dadi in iya a kawo mini Zane dai an kayin sa tun ran gini Ban adawa, tunda rabbana yayai hani Toh akwai nau, babu wanda zai sam mini Tinda baiwa gashi rabbana yayai mini Bani fatan mu tsaya mu dinga kallon kallo Haka Allah ya nufe ni tunda dai har nai tsintuwa Ban da mata wa zamu bawa girma Tunda na kula hakkin su nada dama In zumunci suka so ka baka fama In na bar su fadan wanda zana kama Wasu zunde karshen su yin nadama Tunda kifi ya fahimci masu koma Tunda mata na Arewa basu gulma Dole in nuna ajinsu nada girma Ko ka boye, koma ka bayyana kai ka jiyo Banda Allah wazaya gane hausar yar tsutsuwa
Writer(s): Bello Hassan, Ado Isah Gwanja Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out