Credits
PERFORMING ARTISTS
Prince na kasheep
Performer
Hairat Abdullahi
Lead Vocals
Salim Sadiq
Lead Vocals
Ibrahim Bappah
Background Vocals
COMPOSITION & LYRICS
Hairat Abdullahi
Songwriter
Salim Sadiq
Songwriter
Ibrahim Bappah
Songwriter
PRODUCTION & ENGINEERING
Prince na kasheep
Producer
Lyrics
[Intro]
Prince production
[Verse 1]
Eh, yadda na zaune ba zai ga gari ba
Haka mai so bai ga zama ba
Daga zuciyar yaro babba
Babu in da bai samu guri ba
[Verse 2]
So taimake ni ki ban yarda
Don guna kin fi kuɗi tsada
Kin ga dashen da ki kai mi ni ya yi huda
Na rusuna a gabanki kamar wada
[Chorus]
Ni dai kin min, na gama ƙarƙare zabina
Ke ce farko, ƙarshe kin ji muradina
[Verse 3]
Ke da ganina kin san na gama kamuwa
A rai da jikina sonki yana daɗa yaɗuwa
Tun a mafarki muka kai ga matakin shaƙuwa
Kuma dana farka mu ka ɗora so ya yi ƙulluwa
[Verse 4]
Ba dabara shigar so ba zaka tare shi ba
Akwai larura cire shi ba za ka yi yanzu ba
Ina gadara da ke don ban ga irinki ba
Diri da sura mata ba su ɗara ki ba
[Chorus]
(Ni dai kin min, na gama ƙarƙare zaɓina)
(Ke ce farko, ƙarshe kin ji muradina)
[Verse 5]
Ah, ka zamana turmi sha daka
Labule asirin cikin ɗaka
In da ka kira ni dole zan zaka
Kai mai muƙami ne
[Verse 6]
Kin tafi da zuciyata duka
Dole ne na miki wasu baituka
Cikin amon da zana yo na raka
Kalmomin so ne
[Verse 7]
Na ba ka kaina jininmu da kai ya yi haɗuwa
Taho mu zauna a tare mu ƙare rayuwa
Domin kai min na gama ƙarƙare zaɓina
Kai ne farko ƙarshe ka ji muradina
[Verse 8]
Ku mini uzuri
Ba ni jin bari
Na yi nazari
Abin da haɗari
In dai na bari
Na rasa ta zan shiga damuwa
[Chorus]
Ni ma kai min, na gama ƙarƙare zaɓina
Kai ne farko, ƙarshe ka ji muradina
[Outro]
(Na gama ƙarƙare zaɓina)
Beats Amjad records
Written by: Hairat Abdullahi, Ibrahim Bappah, Salim Sadiq

