Music Video

Music Video

Credits

PERFORMING ARTISTS
Abdull D
Abdull D
Performer
Umar M Sharif
Umar M Sharif
Performer
COMPOSITION & LYRICS
Abdull D
Abdull D
Composer

Lyrics

Tankade dole sai da Rariya
Rariya-Rariya
Rariya-Rariya
Rariya-Rariya
Tankade nayo nasa Rariya
Kece kikazam tsaba zabina a soyayya
Tankade nayo nasa Rariya
Kai ne kazamo tsaba zabina a soyayya
Na tankade soyayya ta nasa Rariya, Rariya
Dan inguji cuta Allah ne mai kariya, kariya
Kuma na dace dan nasamo mai tarbiya, tarbiya
Lafazinta da dadi sam-sam bata ashariya, ashariya
Nazam' gwanin so dole ayimin jiniya
In nataho kiyo dauki kimin tarba ta soyayya
Rariya-Rariya
Nan-nan-nan, nayi nisa a so nai kololuwa, loluwa
Cikin akala damin nan naiyo tsintuwa, tsintuwa
Kai ka zame mini allura na cikin ruwa, cikin ruwa
Nazama mai sa'a samunka a rayuwa, rayuwa
Duniyata yau tadawo sabuwa
Kai kashigo kayo aiki dole inmaka sakayya
Rariya-Rariya
Ayyah! ah ruwan sama inkaga yayi zubowa ai damuna ce
Aure inkaga yai dorewa wannan kauna ce
Kyautar Allah nadayawa naga baiwa baiwa ce
Shi ya hadamu dake kan kauna, ance mundace
In narasa ki a soyayya sai na mace
Koko jiki yabar aiki tunda rabinshi ya tsaya
Rariya-Rariya
A hagu da dama kai naka dubi
Nafadawa iyaye kaine zabi
Littafin so ciki babi-babi
Sunanka yana ciki fannin hubbi
Kowa kagani a cikin littfin gallery dole
Hannunsa akwai mulki, ko-ko sarautar soyayya
Tankade nayo nasa Rariya
Kece kikazam' tsaba zabina a soyayya
Tankade nayo nasa Rariya
Kai ne kazamo tsaba zabina a soyayya
Tankade nayo nasa Rariya
Kece kikazam tsaba zabina a soyayya
Written by: Umar M Shareef
instagramSharePathic_arrow_out

Loading...