album cover
Jarumin Maza
8,691
Worldwide
Jarumin Maza was released on July 6, 2018 by Nedjon Media as a part of the album Tribal Grooves, Vol. 27
album cover
Release DateJuly 6, 2018
LabelNedjon Media
Melodicness
Acousticness
Valence
Danceability
Energy
BPM109

Credits

Lyrics

Ni ne na ki jarumin maza yarje min
In kin guje min a ina za ni je
Jarumin maza, jarumin maza
Jarumin maza
Kunnuwana mai kuke ji ne
Ban aminta ba yaudara ne
Ka ɓoye hali, idonka ashe da kwalli
Ka na da bakin hali wanda ka boye mini
Eh! Babu zato babu tsammani
Rayuwar da na tsinci kaina ni
Rabin jikina kar ki bar ni
Bakin fenti aka yo gare ni
An saka na canja kamanni
Kuma so ake yi ki bar ni
Lokaci daya dubi masoya, mu zama maƙiya
Na gane shirinka a kaina
Ka gusar min da farin cikina
Kuma ka yi nasara ganina
Sai dai kar ka manta haƙƙina
Na sani amma bai bari na
Da sannu wata ran za ka bayyana
Za ka shigo hannu, asiri za ya tonu
Ka shiga ramin karya, za ya kure
Matata kar ki zamo mai mantuwa
Mun daɗe dake a aure mun yi shaƙuwa
Halayyata kin sani tsohuwa ko ko sabuwa
A tsakani na da ke ba zancen cutarwa
Sannu a sannu za ki gane
Masoyinki ni ne
Jarumin maza ne
Ai ya kamata ki gane
Ban yi canjin halina ba
Wahala ba za ta sanya ba
Lokaci ba za ya ƙare ba
Gaskiya za ta fito
Allahu kai nake roko, share hawayena
Zaluncin da anka yi min ka bi min haƙƙina
Tun a duniya ka nuna min na gani da idona
Farin ciki na ya dawo sanyi na raina
Zato nake na yi dacen soyayya mijina
Ashe kai ko ƙi na kake burinka tadda baya na
Allah na tare da ni, shi za ya kare ni
Da sannu za ka shigo hannu a bi min haƙƙi na
Ni ne naki jarumin maza yarje
In kin guje ni ina za ni je
Jarumin maza, jarumin maza
Jarumin maza
Kunnuwana mai kuke ji ne
Ban aminta ba yaudara ne
Ka ɓoye hali, idonka ashe da kwalli
Kana da baƙin hali wanda ka ɓoye mini
Written by: Umar M Sharif
instagramSharePathic_arrow_out􀆄 copy􀐅􀋲

Loading...